Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya buƙaci mabiya addinin islama da ke jihar da su cigaba da nuna dabi’a ta zaman lafiya da kuma son mutane.
Inda ya bayyana aniyar gwamnatinsa na ba wa har tsaro muhimmanci da kuma kare rayukan duk wanda ke zaune a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a saƙonsa na barka da sallah ga al’ummar musulman Najeriya, musamman musulman da ke zaune a jiharsa.
Sanarwar ta fito ne daga hannun mai magana da yawun gwamnan, Mista Daniel Alabrah wacce ya fitar a ranar Laraba.
Ya bukaci musulmai da su yi amfani da wannan lokaci na bikin sallah wajen inganta imaninsu da kuma addu’a kan haɗin kan ‘yan kasar nan.
Karshe, gwamnan ya yi addu’a ga musulmi na kasancewa cikin farin ciki a yayin shagulgulan sallah tare da fatan cigaba mai ɗorewa ga jiharsa ta Bayelsa.