A cikin wata sanarwar da kakakin yaɗa labarai na gwamnan Yusuf Sanda ya fitar, ya ce rushewar ta fara aiki ne nan take, domin Wa’adin milkin shugabannin ya ƙare ne a watan Maris na wannan shekarar, amma gwamnatin da ta gabata ta ƙara musu wa’adin wata uku.
Gwamnan ya umarci shugabannin ƙananan hukumomin da su miƙa duk wasu kayan gwamnati da ke hannunsu zuwa ga shugabannin ma’aikatan ƙananan hukumominsu nan ta ke.
Da ya ke magana kan wannan hukuncin, shugaban ma’aikatan ƙananan hukumomi na jihar, Bala Bako, ya nuna godiyarsa ga tsohon gwamnan jihar, Darius Ishaku, bisa ƙara musu wa’adin mulki da ya yi.
A nasa ɓangaren, tsohon babban sakataren hukumar ƙananan hukumomi da masarautu ta jihar, Bello Yero, ya bayyana cewa yana alfahari da nasarar da shugabannin ƙananan hukumomin suka samu.