Kwamitin Rusau na Gwamnan Kano Eng. Abba Kabir Yusuf ya dirarwa gine ginen da aka yi a daura da Titin BUK a hauren wanki.
A jiya Juma’ar nan ne aka ga Hukumar Tsara birane ta jahar kano KNUPDA ta shafa Jan fenti ga Dogayen gine-ginen da aka yi tare da ba su wa’adin kwance gine-ginen bisa hujjar cewa an yi su akan Badala.
Ko a baya baya nan Kungiyoyin Fararen hula irinsu Good Governance and Change Initiative (GGCI) su kiyasta cewa anyi asarar sama da naira Biliyan 150 daga fara rushe gine-ginen da gwamnati ta ce Tsohon Gwamnan Kano Dr Abdullahi Ganduje ya ba da izini yinsu a wuraren da ba su da ce ba.
Sai dai Gwamna Abba Kabir yusuf ya ce daga fara aikin na rusau, gwamnatin kano tai nasarar Kwato filayenta na Triliyoyin naira