Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da mayar da Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado a matsayin Shugaban Hukumar Sauraron Korafe-korafen Al’umma da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta jihar Kano, domin kammala wa’adinsa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan jihar ta Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.
A baya dai gwamnatin da ta gabata ta Abdullahi Umar Gnaduje ta dakatar da Muhuyi tare da tsige shi daga mukaminsa bayan majalisar dokokin jiha ta ce tana da shakku kan yadda yake gudanar da ayyukansa.
Sanarwar ta bayyana cewa Barista Muhuyi zai koma kan aikinsa ne nan take.