Sabon gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya sha alwashin ƙwato dukkanin kadarorin gwamnati da wasu suka siya a lokacin mulkin gwamnatin da ya gada.
Majiyarmuta rawaito cewar, gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen wata liyafa, da aka shirya domin tarbarsa da shi da mataimakinsa, Idris Gobir. Inda ya ce, kadarorin jihar mallakin al’ummar jihar ne, ba wai na wani ba ne da zai siyar ko ya rabar da su, ba tare da bin hanyar da ta dace ba.
Gwamnan ya kuma buƙaci duk wanda ya san ya amfana daga irin wannan rabon da gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal ta yi, da ya gaggauta dawo da waɗannan kadarorin hannun gwamnati ko kuma a tilasta masa yin hakan.
Gwamnan ya ƙara da cewar, A lokacin yaƙin neman zaɓe ya yi alƙawarin kare mutanen jihar da dukiyoyin su, kuma ba zai kasance cikin masu raba kadarorin jihar ga ƴan baranda ba.
Gwamna Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa ya sauya daga sanin da aka yi masa a baya na mai neman gwamnan jihar. Inda ya ce, “Duk wanda ya ƙi ya dawo da waɗannan kadarorin zai fuskanci fushin hukuma.