Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ya kafa wani kwamitin mutum tara da zai yi bincike domin ganin yadda aka tafiyar da hukumomin jihar Taraba tun daga 2019.
A makon nan ne Gwamna kefas ya sauke dukkanin shugabannin da ke kula da hukumomi da ma’aikatun da Darius Ishaku ya nada a ofis.
Gwamnan ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar a garin Jalingo ta bakin sakataren gwamnati, Cif Gibeon-Timothy Kataps wadda ta bayyana cewar, kwamitin binciken ya na karkashin jagorancin mai binciken kudi, Polycarp Iranius.
Iranius, da ‘yan kwamitinsa mai kunshe da kwararrun ma’aikata, za su duba yadda kudi su ka rika shigowa da kuma fitarsu a cikin shekaru hudun da suka gabata.
Sannan kwamitin zai yi wa gwamnati bayanin kokarin da hukumomin su ke yi, a karshe za su bada shawarar hanyar da za abi domin kawo gyara.