A jiya Alhamis, Gwamnana Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya jagoranci dimbin jama’a domin yin Sallar rokon ruwa, saboda karancin ruwan saman da Jihar ke fsukanta.
Jim kadan bayan idar da sallar, Gwamnan ya ce Jihar na fama da matsanancin fari yayin da damina ta lula, inda ya ce ya zama wajibi a yi sallar don neman taimakon Allah.
Ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da addu’ar domin manoma su sami damina mai albarka ta yadda za su sami amfani mai yawa.
Gwamnan, wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa, Auwal Jatau, ya kuma gode wa Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu da sauran malaman Jihar saboda shirya sallar.