Gwamnatin jihar kano ta miƙa muhimman bayanan gwamnatin ga kwamitin karɓar mulki na jam’iyyar NNPP dake karkashin jagorancin Shugaban kwamitin Dr. Abdullahi Baffa Bichi.
Shugaban kwamitin miƙa mulki na jam’iyyar APC kuma Sakataren gwamnatin jihar kano, Alhaji Usman Alhaji ne ya mika muhimman bayanan a madadin gwamnatin mai barin gado a gidan gwamnatin kano.
Usman Alhaji ya ce, sun Sami fahimta juna sosai wajen gudanar da aiki saboda dukkanin bangarorin magana suke ta yadda za’a ciyar da jihar kano gaba.
A jawabinsa Shugaban kwamitin karɓar mulki na jam’iyyar NNPP Dr. Abdullahi Baffa Bichi, ya yabawa kwamitin miƙa mulkin Saboda yadda suka gudanar da aikin tattara bayanan.
Wannan dai na daga cikin tsare-tsaren shigar sabuwar gwamnati domin kama aiki a ranar litinin mai zuwa 29 ga watan mayun da muke ciki.