Gwamnatin jihar Jigawa ta tabbatar da cewa ta yi nasarar yashe kogin Hadeja a tazarar da ta kai kilomita 60 tare da gina katangar kariya a tsawon kilomita 100 domin magance matsalar ambaliyar ruwa da ake samu a jihar.
Gwamnan jihar, Umar Namadi, ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da ƴan jarida a garin Dutse a wannan mako.
Ya ce sun ɗauki wannan mataki na gaggawa ne ta hanyar samar da mayan motocin yashe kogi, ita kuma Hukumar Raya Kogunan Hadeja Da Jama’are ta samar da karin irin motocin guda biyu domin taimaka wa shirin gwamnatin jihar.
Sannan an samar da kayan aikin cire ciyayi da kan tsuro a gaɓar koguna waɗanda ke toshe hanya su hana ruwa gudu, kuma an rarraba kayan aikin ga ƙungiyoyin sa kai na ƙananan hukumomi goma sha uku.
Gwamnan ya ce baya ga waɗannan matakai na kare afkuwar ambaliyar ruwa, an kuma samar da taki da ingantaccen irin da aka saya da ragin kashi 40 cikin ɗari domin a tabbatar manoma sun samu yabanya mai kyau.
A baya dai ƙididdigar kwamitin yaki da ambaliyar ruwa ta jihar Jigawa ta bayyana cewa wadda aka samu a shekarar 2022, ta shafi ƙananan hukumomi 22 da kuma ƙauyuka 1, 554, ta share gonakin da faɗinsu ya kai kadada dubu 138,422.36, kuma mutane 130 suka rasa rayukansu a faɗin jihar.