Hukumar kula da Asibitocin jihar Kano ta amince da tuɓe Shugabannin Asibitoci uku na jihar.
Shugaban asibitocin da abun ya shafa sun haɗa da na Babban Asibitin Imam Wali da na Asibitin Mafitsara na Abubakar Imam, sai kuma Asibitin haihuwa na Nuhu Bamalli. Inda aka maye gurbinsu da wasu nan take.
Wani rahoto ya bayyana cewa Babban Sakataren Hukumar Dr Mansur Nagoda ya kuma amince da dakatar da dukkanin likitoci da ma’aikatan jinya da suke kan aiki a wuni da kuma daren ranar Lahadi 30 ga watan Yulin da ya gabata.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar, Samira Sulaiman ta raba wa manema labarai.
Sanarwar ta ce an yanke hukuncin ne a gaggauce, duba da sakacin ma’aikatan da aka dakatar wajen gudanar da ayyukansu, inda suka bar marasa lafiya a hannun ɗalibai masu neman ƙwarewa.
Babban sakataren hukumar ya gargadi sauran ma’aikata akan irin wannan sakacin, inda ya ce ba za su lamince shi ba.