Gwamnatin jihar Kano ta haramta manna fastoci na siyasa da na tallace-tallace a jikin gine-ginen gwamnati da na masu zaman-kansu a faɗin jihar.
Sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana haka cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Gwamnatin jihar ta ce za ta kafa wata hukuma da za ta tabbatar da bin sabuwar dokar a wani mataki na tsaftace bangwaye da sauran gine-gine daga fastocin siyasa a jihar.
Sanarwar ta kuma buƙaci masu talla da su yi amfani da allunan talla da sauran hanyoyin tallata haja wajen gudanar da tallace-tallacensu.
Gwamnan jihar ya umarci jami’ai daga ma’aikatar muhalli da hukumar kashe gobara ta jihar da su riƙa zagayawa titunan birnin domin yage fastocin da aka manna na siyasa da na tallace-tallace.