Home » Gwamnatin Kano Ta Mika ‘Yan Cirani 49 Ga Iyalansu

Gwamnatin Kano Ta Mika ‘Yan Cirani 49 Ga Iyalansu

by Abubakar Kankara
0 comment

Kwamishinar Ma’aikatar Jin Kai Da Rage Talauci A Tsakanin Al’umma ta jihar Kano Hajiya Amina Abdullahi Sani ta jagoranci taron mayar da ‘yan cirani ga iyalansu.

‘yan ciranin sun hada da yara ƙanana 21 da iyayensu da kuma wasu matasa, wadanda suka je kasar Ghana neman arziki,

A yayin wannan tafiya tasu ne dai ‘yan ciranin suka haɗu da ƙalubalen hukumomin kasar Ghana, inda aka kamosu a matsayin wadanda suka shiga kasar ba bisa ƙa’ida ba.

Bayan an kawo su jihar Lagos ne, gwamnatin ta Kano ta tura tawaga a karkashin jagorancin kwamishina Hajiya Amina Abdullahi Sani wadda ta dawo da su gida jihar Kano.

Da take jawabi ga ƴan ciranin da iyalansu, kwamishina Hajiya Amina Abdullahi Sani ta tunatar da su hadarin da ke cikin irin wadan nan tafiye-tafiye.

“Alhamdulillah yau rana ce ta farinciki, yau rana ce da nake sauke nauyin da maigirma gwamna ya doramin na wadan nan iyalai da muka je muka dakkosu daga Legas, ba abinda zamu ce da Allah sai godiya, kuma muna godewa mai girma gwamna da ya tura mu, muka je  muka taho da wadannan yara tun daga Legas muke dawainiyar su.

“Yau kwana wajen na tara ke nan muka kawo su jihar kano, muka zauna aka duba lafiyar su, muka tabbatar ba su dakkomana wata cuta ba. A yau mai girma gwamana ya sallami wadannan iyali da ya musu tagoma shi, wajen iyalai 13 ko wacce za kaga daga mai ‘ya’ya biyar sai mai shida har bakwwai, ta ɗebesu ta tafi Ghana da su wajen fatauci kokuma neman wani arziki”.

“Alhamdullah, kowane iyali gwamana ya basu buhun shinkafa mai kilo 25 guda 4 da kuma buhun masara mai kilo 50 guda 2, Ya kuma basu naira dubu dari da za su je su rike kansu”.

Shima Kwamishinan yada labarai wanda ya wakilci gwamnan Kano wajen taron, Baba Halilu Ɗantiye, ya bayyana jindadin gwamnati bisa nasarar dawo da ƴan ciranin gida cikin aminci.

“Farko muna yiwa Allah s.w.a godiya da aka ɗebo waɗan nan yara da mata da matasa daga Ghana zuwa Legos, daga Lagos zuwa Kano. Mai girma gwamana sakonsa daya shi ne cewa, su kula da kansu sosai ba irin wannan tafiya, su je su saka kansu cikin matsala ba, su jawowa kasa da jihar Kano matsala”.

“Mai girma gwamna farincikinsa shi ne, ba wai laifi suka yi ba, ba wani abun kunya suka yi ba, ba wani laifi aka kama su da shi ba, ka wai dai nema ne ya kai su”.

“A nan kasar ma duk ana irin wannan, za ka ga an debo mutane daga wannan jihar ace ba ƴan nan jihar bane ballantana kasa. Saboda haka, kano ba wani abun kunya suka yi ba ballantana ace za a kyamace su”.

“Ba maganar kyama, kuma ita kwamishina ga shi ta jagoranci ba su wannan tallafi, ta yi musu jawabi tare da gargadi a matsayinta na uwa”.

Kwamishinar Jinkai da Rage Talauci ta Jihar Kano ta gargadi ‘yan ciranin da kada su bari a sake kamo su, domin duk wanda aka kama zai fuskanci fushin hukuma.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?