DAGA: YASIR ADAMIU
Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta kaddamar da sake dawo da shirin fitar da dalibai kasashen ketare domin karo ilimi, inda a wannan karo dalibai 1001 za su amfana da wannan shiri na zuwa makarantun kasashen duniya don yin karatun digiri na biyu.
A wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya raba wa manema labarai, ya ce rukunin farko na wadannan dalibai su 150 za su bar Najeriya a yau Juma’a zuwa kasashen da za su yi karatunsu.