Home » Gwamnatin Kano ya ayyana yau a matsayin hutu ga ma’aikata

Gwamnatin Kano ya ayyana yau a matsayin hutu ga ma’aikata

by Anas Dansalma
0 comment
Gwamnatin Kano ya ayyana yau a matsayin hutu ga ma'aikata

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ayyana yau Laraba 4 ga watan Oktoba, a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin ciki gida, Baba Halilu Dantiye, ya fitar.

Gwamnan ya buƙaci al’ummar jihar nan da su yi amfani da lokutan bukukuwan mauludin domin yin tunani a kan koyarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama tare da aiwatar da su cikin harkokinsu na yau da kullum.

Ya kuma buƙaci jama’a da su riƙa yin addu’a domin samun zaman lafiya da ci gaba a Kano da Nijeriya baki ɗaya.

A ƙarshe ya yi addu’ar Allah ya fitar da ɗaukacin Musulmi daga cikin mawuyacin halin da ake ciki, tare da samun damina mai albarka.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi