Gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya bayyana kudurin sake gina katafaren shatale-talen gidan gwamnatin jihar da aka rusa a kwanakin baya a daura da gadar Naibawa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin da yake gana wa da mai zanen shatale-talen ‘Golden Jubilee Kaltume Ghana.
Ya ce bayan gudanar da cikakken bincike, wurin ya dace da zanen kuma ba zai haifar da wani kalubalen tsaro ba, ya kuma sake tabbatar wa ‘yan jihar cigaba da samar da ayyukan more rayuwa masu inganci.