Sanata Ali Ndume daga jihar Barno ya ce ko kaɗai faɗuwar darajar Naira ba ta shafi gwamnatin tarayya ba, sai ma samun ƙarin kuɗin shiga da take yi domin ganin ta kai ga samar da kuɗin kasafin bana.
Wannan na zuwa ne a lokacin da masana da dama na cigaba da alaƙanta tsadar rayuwa da ake fuskanta da tashin farashin Dalar saboda faɗuwar darajar Naira da rashin albarkarta wajen siyan kayan masarufi.
Sai dai sanatan ya ba da dalilin cewa an tsara kasafin kuɗin bana wanda shugaba Bola Ahmad Tinubu ya gabatar wa da majalisar a kan darajar Dalar Amurka ta la’akari da cewa Najeriya na samun kaso mafi yawa na kuɗin shigarta ne daga man fetur wanda ake fita da shi waje da kuma ake siya da Dala.
Ya kuma ce abin da al’umma ba su fahimta shi ne cigaba da tashin Dala na nufin gwamnatin tarayya za ta samu ƙarin kuɗin naira da za ta kashe wajen ayyukanta.
Sannan ya ƙara da cewa har yanzu man fetur na cikin abubuwan da ake nema a kasuwar duniya wanda hakan ke ƙara ba wa gwamnatin tarayya damar cigaba da samun kuɗin shiga matuƙar farashin Dala ya cigaba da ƙaruwa.