A wani yunkurin gwamnatin kasar nan na bunkasa amfani da Gas a matsayin makamashin da motoci za su yi aiki da shi, Shugaba Bola Tinubu ya amince da wani shirin gwamnatin tarayya don cimma wannan manufa.
Wannan wani mataki ne don rage radadin janye tallafin mai, ta hanyar rage farashin makamashi.
Manufar shirin ita ce sauya fasalin sufuri a kasar, da samar da motoci 11,500 masu amfani da gas, da kayayyakin sauya injinan mota 55,000 daga fetur zuwa gas.
A wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar, ta ce burin shirin shi ne yawaita amfani da gas din a fadin Nijeriya a matsayin makamashin da motoci ke amfani da shi.
Abubuwan da shirin ya kunsa sun hada da horarwa, da hada kayayyakin ayyukan gas, wanda a farko zai fuskanci harkar sufurin jama’a da na dalibai, don rage kudin motacin haya ga jama’a.