Gwamnatin Tarayya ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na bayar da kasonta ga kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta hanyar ba da cikakken kudin gudummuwarta na shekarar 2023 baki daya.
Babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen kasar, Ambasada Adamu Ibrahim Lamuwa, ne ya tabbatar da hakan a gefen taron majalisar zartarwa ta AU karo na 43 a birnin Nairobi na kasar Kenya.
Ambasada Lamuwa ya yi maraba da yadda aka yi la’akari da yanayin tattalin arzikin kasashen Afirka a halin da ake ciki, wajen tsara kasafin kudin kungiyar da kuma yadda kowa ce kasa za ta bayar da gudummarwata.
Ya kuma jaddada bukatar bin ka’idojin bincike kan kudin da ake kashewa a kungiyar don tabbatar da gaskiya da rikon amana.