Home » Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Ɗage Fara Kidayar Jama’a

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Ɗage Fara Kidayar Jama’a

by Anas Dansalma
0 comment

Majalisar zartarwar ta ƙasa a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta amince da bukatar dage ranar fara aikin kidayar jama’a da gidaje a kasar nan.

Babban jami’in yada labarai Na fadar shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana dalilan sauye ranar fara aikin ƙidayar jama’ar.

A cewar Garba ShehuN, bayan da hukumar zaɓe ta dage zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha zuwa ranar 18 ga watan nan, hukumar kidayar ta nemi gwamnati ta ba ta damar dage kidayar jama’a da gidaje daga ranar 29 ga watan Maris zuwa karshen watan Mayu.

Malam Garba Shehu ya kuma ce majalisar kolin kasar nan ta amince a ba wa hukumar kidaya ta kasa makudan kudaden da za a yi amfani da su don sayen wata na’ura da za ta taimaka wajen yin kidayar.

Garba Shehu ya ce wannan shi ne karon farko da za a yi kidaya ta hanyar amfani da na’u’rorin zamani a ƙasar nan. Ya kara da cewa jami’ai za su yi amfani da kwamfuta, sannan na’urar z ata yi amfani da tauraron dan’adam.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?