Ministar ƙwadago da ayyukan yi Nkiruka Onyejeocha, ta ce gwamnatin tarayya ta yi nasarar cika alƙawuran da ta yi wa ƙungiyar ƙwadago a watan Oktoban bara da kashi 90 cikin 100.
Ta ce yanzu lokaci ne da ya kamata ƙungiyoyin ƙwadago su tallafa wa gwamnatin tarayya.
Minstar dai ta bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ta yi da wata ƙafar talabijin, inda ta kafa hujja da cewa shi kansa shugaban ƙwadago na ƙasa, Joe Ajaero, ya tabbatar da cewa zanga-zangar da suka yi ba a kan yarjejeniyarsu da gwamnatin tarayya ba ce, tace ya ce sun yi zanga-zanga ne a kan matsalar tsadar kayan masarufi.
Ministar ta ce matsalar tsadar kayan masarufi na cikin manyan abubuwa da gwamnatin Tinubu take ƙoƙarin magancewa.
Ta kuma roƙi ‘yan Najeriya kan su ƙara haƙuri domin nasara na zuwa nan gaba kaɗan.