Gwamnatin Tarayya ta ce har yanzu ba a cim ma matsaya ba, a kan matakan da za a dauka idan an janye tallafin fetur a tsakiyar shekarar nan.
Majiyarmu ta rawaito cewa karamin Ministan tsare-tsaren kasa da kasafi, Clement Agba ya yi bayanin nan ne bayan taron ‘Yan majalisar zartarwa a jiya Laraba.
Clement Agba ya amsa tambayoyi daga wajen manema labarai a fadar shugaban kasa bayan Muhammadu Buhari ya jagoranci taron Ministocin. Ministan ya nuna kwamitin da Farfesa Yemi Osinbajo yake jagoranta ya yi kusan shekara daya yana aiki, amma dai ba a kai ga cin ma matsaya ba.
Agba ya shaida wa manema labarai cewa suna sa ran kwamitin da yake aiki da Gwamnonin jihohi zai yanke shawara kan matsayar da za a dauka.
Baya ga haka, Agba ya ce jam’iyyu da ƙungiyoyin kwadago, da kungiyoyin matasa da mata, da malaman addini da sarakuna duk suna da ta-cewa.