An tabbatar da mutuwar mutane takwas a Rugange da ke ƙaramar Hukumar Yola ta Kudu, a jihar Adamawa, sanadiyar kifewar kwale-kwale a ƙarshen makon nan, kuma wasu mutane 15 sun ɓace a ruwa ba a gan su ba.
Kwale-kwalen na ɗauke da fasinjoji 23 a lokacin da ya kife a ruwa sanadiyar wata gagarumar iska da ta rutsa da su.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ya faɗa cewa a cikin gawarwakin mutane takwas da aka tsamo, akwai mata 6 da maza biyu. Kuma ya bayar da tabbacin cewa nan kusa zai yi ƙarin bayani kan halin da ake ciki game da hatsarin kwale-kwalen.
Wani mazaunin yankin mai suna Mahmud wanda tare da shi ake aikin ceton, ya faɗa wa manema labarai cewa mummunan hatsarin ya faru ne saboda mawuyacin halin da kwale-kwalen ya samu kansa a ciki a lokacin da iskar ta taso, kuma yace har ma da rashin yin amfani da irin ƴan rigunan nan da ake kira life jacket masu hana mutane nitsewa a ruwa.
Yace shekaru talatin ke nan yana zaune a yankin amma bai taɓa ganin mummunan hatsarin kwale-kwale irin wannan ba, sannan ya yi kira ga gwamnati ta samar wa al’ummar yankin mafita mai ɗorewa, a cewarsa, dole ne mutane su shiga kwale-kwale don zuwa kasuwa da gudanar da sauran harkokinsu na rayuwar yau da kullum, saboda hanyar mota ɗaya da suke amfani da ita ta kwararraɓe.