Home » Hukumar DSS sun bankado wani shiri na tada-zaune-tsaye a Najeriya

Hukumar DSS sun bankado wani shiri na tada-zaune-tsaye a Najeriya

by Anas Dansalma
0 comment
Hukumar DSS sun bankado wani shiri na tada-zaune-tsaye a Najeriya

Mai magana da yawun Hukumar DSS ta jami’an tsaron farin kaya, Dokta Peter Afunanya ya fitar da sanarwar cewa sun gano wasu mutane a sassan Najeriya daban-daban wadanda ke neman tada zaune-tsaye ta hanyar yin amfani da mummunar zanga-zangar da za su shirya don su ɓata wa gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro suna tare da zubar mutunci saboda wahalhalun da ake ciki sanadiyar tsadar rayuwa.

Bayanan sirri sun nuna cewa a cikin masu kitsa wannan makircin har da wasu ƴan siyasa da ke ƙoƙarin shigar da wasu shugabannin ɗalibai da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba, da ƙungiyoyin wasu ƙabilu, da matasa, da kuma waɗanda ke ganin an ha’ince su, ba a kyautata musu ba, duk su haɗu su tada fitinar.

A halin da ake ciki Hukumar ta DSS ta ce ta gano shugabannin tafiyar kuma tana ci gaba da sa musu ido don ta hana su jefa ƙasar cikin ruɗani.

Game da wannan labari an buƙaci shugabannin jami’o’i, da na manyan makarantu su hana ɗalibai aikata abubuwan hargitsa ƙasa da hana jama’a zaman lafiya. Suma iyaye an yi kira gare su, su tsawata wa ƴaƴansu da waɗanda ke ƙarƙashin kulawarsu, kuma su raba su da biye wa masu son kai su, su baro su ta hanyar ingiza su su yi abubuwan da za su saɓa wa doka da oda.

A yayin da Hukumar DSS tace tana sane da ƙoƙarin da gwamnati ke yi da kuma jajircewarta wajen magance wa ƴan ƙasa halin tsananin rayuwar da suke fuskanta, a gefe ɗaya kuma tana gargaɗin masu son yi wa aikin tsaro zagon ƙasa, tana mai cewa su sake tunani.

Hukumar tace saboda haka babu abinda zai hana ta yin amfani da bulalar doka akan waɗanda ke ƙoƙarin shirya makircin na tada zaune tsaye a ƙasa.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?