Home » Hukumar DSS Ta Kame Wasu Masu Sana’ar POS a Jihar Ondo

Hukumar DSS Ta Kame Wasu Masu Sana’ar POS a Jihar Ondo

by Anas Dansalma
0 comment

Jami’an Hukumar Yaki da Masu Iya Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa, (EFCC) sun kama wasu masu sana’ar POS a ƙarshen wannan makon da ya gabata.

An kama mutanen ne a Jihar Ondo saboda zarginsu da badaƙalar sayar da sabbin kuɗaɗe a kan farashi mai ɗan karen tsada.

Manema labarai sun gano cewa jami’an hukumar wadanda ke sanye da fararen kaya sun yi wa Akure, babban birnin Jihar kawanya ne a kokarinsu na kama mutanen a manyan kasuwannin birnin.

Bayanai dai sun nuna yawancin mutanen sun rika cin karensu ba babbaka, inda suka rika sayen takardun kudaden daga hannun bankuna suna sayar da su ga mutane a kan farashi mai tsada.

Kai samamen ya biyo bayan wasu bayanan sirri da suka samu ne kan yadda galibin masu sana’ar ke boye sabbin kudaden don kuntata wa jama’a.

 Jami’an sun yanke shawarar yi musu dirar mikiya ne musamman a cikin manyan kasuwannin birnin, inda a nan ne wannan dabi’ar ta fi kamari.

Daya daga cikin jami’an yace zasu shafe tsawon mako guda suna wannan aikin, domin su kawo gyara kan yadda kudade za su wadata a Jihar da ma kasa baki daya.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?