Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta fara bin diddigin Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC mai mulki na kasa, kan gazawarsa wajen bayyana inda kudade sama da Naira biliyan 32 da jam’iyyar ta tara daga sayar da fom din takara a zaben 2023.
Wata majiya a hukumar EFCC ta tabbatarwa da manema labarai cewa, jami’an EFCC sun ziyarci gidan Abdullahi Adamu, yayin da ya mika takardar murabus dinsa ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila.
Jami’an EFCC sun ziyarci gidansa da ke kan Ali Akilu Crescent, da ke fadar Aso Rock Villa tare da takardar izinin bincike da misalin karfe 8 na dare.