Home » Hukumomin jihar Kano sun kaddamar da dokar ta-ɓaci game da satar waya

Hukumomin jihar Kano sun kaddamar da dokar ta-ɓaci game da satar waya

by Anas Dansalma
0 comment
majalisar dokokin jihar Kano ta nuna damuwa kan matsalolin satar waya da sane da shan miyagun kwayoyi da ma waɗansu laifukan da ke barazana ga zaman lafiyar jihar.

Hukumomi a jihar Kano sun ƙaddamar da dokar ta-ɓaci game da satar waya da kuma wasu laifukan da ake aikatawa a birnin.

majalisar dokokin jihar Kano ta nuna damuwa kan matsalolin satar waya da sane da shan miyagun kwayoyi da ma waɗansu laifukan da ke barazana ga zaman lafiyar jihar.

A wata mahawara da shugaban masu rinjaye na majalisar ya gabatar, ‘yan majalisar sun amince kan cewa akwai buƙatar a gaggauta magance matsalar kafin ta yi ƙamari.

Majalisar dokokin ta kuma amince da wani ƙuduri da ya buƙaci gwamnatin jihar ta dauki dukkan matakan da suka kamata domin hukunta waɗanda aka kama da laifi.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?