Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta tabbatar da cewa a shirye take ta damƙa kwafen bayanai da dukkan kayan da kotu ta bayar da umarni ga jam’iyyu ko ‘yan takarar da ke ƙorafi kan zaɓen ranar 25 ga Fabrairu, domin su yi nazarin da su ke so su yi.
Shugaban hukumar , Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka, lokacin da ya karɓi tawagar lauyoyin jam’iyyar LP bisa jagorancin Babban Lauya Livy Uzoukwu.
Tawagar ta lauyoyin na LP dai sun ziyarci Hedikwatar Hukumar Zaɓe ne a Abuja.
Yakubu ya tabbatar masu da cewa ya karɓi wasiƙar da jam’iyyar LP ta aika masa a ranar 6 ga wannan watan, wadda ta sanar da shi cewa lauyoyinta za su kai ziyara INEC domin duba kayan zaɓe.
Ya ce wasiƙar na ɗauke da ƙarin bayanin sanar da shi cewa ya sanar da Kwamishinonin Zaɓe na INEC da ke a kowace jiha, cikin jihohi 36 na faɗin ƙasar nan.
Wasiƙar dai ta nemi hukumar INEC ta umarci Kwamishinonin Zaɓe na jihohin su damƙa wa jam’iyyar LP bayanai da kayan da ta ke buƙata domin gabatar da bayanan ƙarar ta a kotu.