Sojojin da ke mulki a jamhuriyyar Nijar sun kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum sun hana jami’ai daga kungiyar Tarayyar Afirka da ECOWAS da Majalisar Dinkin Duniya zuwa ƙasar.
Wannan na zuwa ne cikin wata wasika daga Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar da aka aike wa wakilan waɗancan ƙasashe wanda ake kallo a matsayin martani na kaucewa duk wani yunkuri ne na diflomasiyya.
Sojojin sun ce “Fushin da ‘yan kasa suke yi a yanzu da kuma tarzomar da suka yi sakamakon takunkuman da ƙungiyar ECOWAS ta sanya musu ne, ya sa suke ganin yanayi ziyarar tasu sam bai dace ba, saboda dalilai na tsaro,”
Tuni dai shugaban Nijeriya Bola Tinubu kuma shugaban ƙungiyar na ECOWAS ya bai wa Babban Bankin Kasar nan umarnin sanya karin takunkumai na kudi ga ƙasar ta Nijar.
Shi ma kakakin shugaban ƙasar nan, Ajuri Ngelale, ya ce a ranar Alhamis ne shuwagabannin ƙasashen ƙungiyar ECOWAS za su bayyana karin hanyoyin da za su bi wajen ganin an shawo kan matsalar siyasa ta ƙasar.