Jami’an tsaro sun zagaye wani gida da ake zargin jami’iyyar PDP mai mulki a Jihar Adamawa ta jibge takardun zaben da aka dangwale na sakamakon zaben jabu a ciki.
Majiyar mu ta gano yadda sojoji da hadin gwiwar ’yan sanda suka rufe hanyar shiga gidan, domin gudanar da bincike unguwar Dougireia a kwaryar birnin Yola da ke Adamawa.
Ita ma ’yar takarar gwamnan jihar a APC, Aishatu Dahiru Binani ta halarci harabar gidan tare da magoya bayanta, kafin ta roke su su bar wajen.
Wata sanarwa da kwamitin yakin neman zaben Binanin, dauke da sa hannun shugaba Martins Yanatham Dickson, ta nuna damuwarta da lamarin, inda ta ce abokin karawarta na PDP, Gwamna Ahmadu Fintiri da ke neman tazarce ne ke amfani da gidan don aikata magudin zabe.
Sai dai wata sanarwa da Babban Daraktan Yada Labaran Gwamnan, Solomon Kumangar ya fitar, ta musanta zargin.
A cewarsa, suna amfani da gidan ne don tattara bayanai da sa ido kan zaben, ba abin da Binanin ke yadawa ba.