Jam’iyyar NNPP ta mayar da martani ga alkalan da suka yi hukunci kan zaɓen gwamnan jihar Kano da aka yi a baya-bayan nan da suka ayyana magoya bayan jam’iyyar da ‘yan daba waɗanda suka yi wa rayuwarsu barazana.
Jam’iyyar ta ce waɗannan kalamai ba gaskiya ba ne kuma cin zarafi ne mambobin jam’iyyar.
Wannan martani ya fito ne daga bakin Odita na jam’iyyar NNPP ta ƙasa, Ladipo Johnson, wanda ya nuna rashin jin daɗinsa game da wani sashe na kamalaman mai shari’a Benson Anya, wanda ya muzanta ‘ya’yan jam’iyyar tasu.
Oditan ya ce ba za su bar wannan al’amari ya wuce a banza ba, za su ɗau duk wani mataki da ka iya kai wa ga maƙa Hukumar Ɗaukar Alƙalai da Ladabtar da Su kan waɗancan kalamai da alƙalan suka yi.
Ya ce sam waɗancan kalamai ba su kamata a ji su daga bakin alƙalan ba.
A ƙarshe ya nuna fatansa na samun adalci a kotun da ɗaukaka ƙara domin tabbatar wa da al’umma ƙarfin guiwar da suke da shi a kan matsayin kotuna da kuma dimokraɗiyya.