Jigawa: Hukumomin Shari’a Sun Sallami Wani Alƙali Saboda Karɓar Rashawa

Hukumar shari’a ta jahar Jigawa ta kori wani Alƙalin kotun shari’ar addinin musulinci a Birnin Kudu ,mai shari’a Safiyanu Muhammad Dabi, bisa laifin karɓar cin hancin naira dubu Hamsin (50,000) daga hannun wani mai ƙara.

Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yaɗa Labarai kan harkokin shari’a na jahar , Abbas Rufa’i Wangara ya sanya wa hannu tare da rabawa manema labarai a birnin Dutse babban birnin jahar Jigawa.

Wangara Ya kara cewa Alƙalin ya karɓi kuɗi naira dubu 50,000 ne a matsayin cin hanci a lokacin da wanda ake ƙara ya bayyana a gaban Alƙalin.

Sanarwar ta ƙara da cewa, biyo bayan tattaunarwa mai zurfi da hukumar kula da harkokin shari’a , a taron ta karo na 170 ne ta yanke shawarar dakatar da Alƙalin.Kazalika hukumar ta gargaɗi ma’aikatan ta da su guji duk wani nau’in cin hanci da rashawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *