Wata kotun majistare a jihar ta tura basaraken ƙauyen Ode a ƙaramar hukumar Akure ta Arewa, Oba Adewale Boboye, gidan gyaran hali, bisa laifin rusa wani gini da lalata bishiyoyi da amfanin gona, ba bisa ƙa’ida.
An bayyana ginin da ya rusa mallakin cocin Apostolic ce, wacce ke akan titin hanyar Ado Ekiti, a yankin Igoba, Akure.
An gurfanar da shi gaban kotun ne kan tuhumomi shida waɗanda suka ginu akan aikata ɓarna.
Mai shigar da ƙara, Ajiboye Babatunde, ya bayyanawa kotun cewa, basaraken da wasu a tsohuwar cocin Pastorate and Laity of The Apostolic, Najeriya, sun haɗa baki domin aikata laifin.
Sai dai basaraken, ta hannun lauyansa Adeola Kayode, ya musanta zarge-zargen da ake masa, inda ya buƙaci kotun da ta yi rangwame wajen yanke hukuncinta. Da ta ke yanke hukuncinta, alƙaliyar kotun, majistare Bukola Ojo, ta yanke masa hukuncin shekara 10 a gidan kaso, bayan ta same shi da laifi kan tuhumar da ake masa. Kotun ta yanke a biya diyyar N5m ga mai shigar da ƙara, bisa rusa katangar da lalata bishiyoyin dabinon da sauran amfanin gonan