An ja hankalin gwamnatin Kaduna kan rahotannin dake zargin cewa waɗansu suna ta sayar wa mutane fom ɗin cin gajiyar kayan tallafi da sauran abubuwan taimakon da gwamnati ke bai wa mafiya rauni a cikin al’umma.
Gwamna Uba Sani ya yi tir da Allah wadai da masu aikata abubuwan rashin sanin ya kamata, sannan kuma yana mai sanar da jama’a cewa babu wani fom ɗin da ake sayarwa a duk fadin jihar da sunan cin gajiyar tallafin ko kuma yin rajistar samun wani taimako.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Muhammad Shehu babban sakataren yada labaran jihar ya sanyawa hannu.
Muhammad Shehu yace jihar ta himmatu wajen tabbatar da cewa tallafin ya kai ga ga wadanda za su amfana tare da kafa kwamitin jin kai don samar da hanyoyin da za a raba kayan abincin yadda ya dace a jihar .
Gwamna Uba sani ya yi kira ga mazauna Kaduna da su tuntubi kananan hukumominsu domin samun bayanai.