Home » Kaduna: PDP Ta Gudanar da Zanga-zangar Ƙin Amincewa da Sakamakon Zaɓe

Kaduna: PDP Ta Gudanar da Zanga-zangar Ƙin Amincewa da Sakamakon Zaɓe

by Anas Dansalma
0 comment

Jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna ta gudanar da zanga-zangar lumana a babban birnin jihar domin neman a ayyana dan takararsu Isah Ashiru Kudan a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

A ranar Litinin din da ta gabata ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben.

Uba Sani ya samu kuri’u 730,002, sai babban abokin hamayyarsa – Isah Ashiru na jami’iyyar PDP – ya samu kuri’u 719,196.

To sai dai jamiyyar PDP ba ta gamsu da sakamakon ba, masu zanga-zangar wadanda galibinsu mata ne sanye da bakaken kaya, sun yi zanga-zangar zuwa sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya reshen Jihar Kaduna.

Wadanda suka jagoranci zanga-zangar akwai tsohuwar Ministar Muhalli, Laurencia Mallam da tsohuwar shugabar mata ta PDP a jihar, Aishatu Madina Inda Suka yi Allah-wadai da ayyana uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben da INEC ta yi, tare da cewar ba shi ne muradin al’ummar Jihar Kaduna ba.

 Madina ta bayyana cewa, bayanan da aka dora a na’urar sakamakon sakamakon INEC na IReV sun nuna cewa PDP ce ta lashe zaben gwamna a Kaduna.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi