Kamfanin rarraba wutar lantarki na KEDCO ya bayyana cewa matsalar da wasu turakun watu dake tunkudo wutar lantarki daga babban tashar samar da wutar dake shiroro ne yasa ake fuskantar matsalar rashin wutar lantarki a jihar kano Jigawa da kaduna.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban sashin yada labarai da hulda da jama’a na kamfanin KEDCO Sani Bala Sani ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikewa manema labarai a Kano.
Sanarwar ta baiwa al’ummar jihohin Kano Jigawa da Kaduna tabbacin zasu saki wutar lantarkin da zarar an kammala gyaran da ake yi a wannan rana.
KEDCO sun hakurkurtar da al’umma bisa matsalar da aka samu ta daukewa wutar lantarki a Wadancan jihohi.
Idan za’a iya tunawa muhasa ta rawaito a yan kwanakin al’ummar jihohin Kano Jigawa da kaduna suna fuskantar matsalar rashin wutar lantarkin wanda hakan ya kawo tsaiko a al’amura da dama