An yi kira ga masu ruwa da tsaki a matakin farko da su gaggauta fara wayar da kan al’umma kan shirin kiyaye afkuwar annobar ambaliyar ruwa a yankunansu.
Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa wato NEMA ta kaddamar da shirin wayar da kan al’umma na daukar matakin kariya daga faruwar annobar ambaliyar ruwa, wadda ta kassara rayuwar mutane da dama a yankin arewacin kasar nan a damunar bara.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban hukumar ta NEMA mustafa Habib yayi kira ga masu ruwa da tsaki a matakin farko da su bai wa hukumar hadin kai wajen wayar da al’umma kan irin matakin da za su dauka a matsayin kariya daga faruwar ambaliyar ruwa.
Sakataren gwamnatin jahar Kano Abdullahi baffa Bichi wanda ya wakilci gwamna Abba Kabir Yusuf a wajen taron, ya bayyana godiya ga hukumar ta NEMA da ta zabi jahar kano don kaddamar da wannan shiri.
Taron dai ya samu halartar limamai da masu unguwanni da kuma shuwagabannin kananan hukumomi da saura masu ruwa da tsaki.An gabatar da taron ne a dakin taro na coronation hall dake fadar gwamnatin jahar Kano.