Kotun ɗaukaka ƙara da ke zaman a babban birnin tarayya Abuja ta bayyana tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna kuma dan takarar APC a matsayin wanda yai nasara a zaben gwamnan jihar Kano da aka gudanar a ranar 18 ga watan maris da ya gabata.
A hukuncin da ta yanke, Kotun ta yi watsi da ƙarar da gwamna mai ci, Abba Kabir Yusuf na jam’iyya NNPP ya ɗaukaka yana ƙalubalantar hukuncin kotun sauraron ƙorafin zaɓen ta jihar Kano.
A ranar 20 ga watan Satumba ne kotun sauraron ƙorafin zaɓe ta jihar Kano ta ce Gawuna ne ya lashe zaɓen.
Inda kotun ta ce ba za a sanya ƙuri’u dubu 165 da dari 663 da aka kaɗa wa Abba Kabir cikin lissafi ba kasancewar babu sa hannu ko tambarin hukumar zaɓe a jikinsu.
1 comment
Allah yatabbatar mana da alkhairi