Home » Kano: Kotun sauraren kararrakin zabe ta yi watsi da karar da APC ta shigar gabanta

Kano: Kotun sauraren kararrakin zabe ta yi watsi da karar da APC ta shigar gabanta

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
Kano: Kotun sauraren kararrakin zabe yi watsi da karar da APC ta shigar gabanta

Kotun sauraren kararrakin zabe ta Majalisar Dokokin Jiha da ke zamanta a Kano, ta yi fatali da karar da jam’iyyar APC da dan takararta Dokta Aliyu Musa Aliyu Kibiya suka shigar a gabanta na kalubalantar nasarar dan majalisa mai wakiltar Rano, Kibiya da mazabar tarayya ta Bunkure a majalisar wakilai ta kasa, Kabiru Alhassan Rurum yayin zaben 2023.

Wata majiya ta ruwaito cewa kotun a ranar ta bayyana cewa masu korafin ba su iya gabatar da wasu kwararan hujjoji a gaban kotun ba domin tabbatar da ikirarin da suka yi kan wanda ya lashe zaben.

Kotun ta jaddada cewa sun kuma gaza wajen bayar da shaida kan zaben 2023 kamar yadda suka yi zargin.

Sai dai kotun ta bai wa masu korafin wa’adin makonni biyu su daukaka kara kan hukuncin da ta yanke idan ba su gamsu da shi ba.

Hukuncin kotun dai shi ne hukunci na farko da aka yanke tun bayan babban zaben 2023.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?