Kwamishinan lafiya anan jihar kano Dr. Abubakar labaran Yusif ya kaddamar da rukakafin cutar mashako wanda aka ansami bullar cutar a wasu kananan hukumumin jahar kano.
Kwamishinan yace Bayan anga bullar cutar a kano sun bazama wajen ganin an tabbatar da an magance wannan cutar
Wanda a dalilin haka aka samar da asibitoci guda biyu wajen magance cutar mashako a jahar kano
Sannan ya ƙara da cewa dukanin wanda suka kamu da wannan cuta ta mashako anabin yan uwa da masu jiya har gidaje ana basu rigakafin wannan cutar.
Kawo yanzu jihar kano tasamu wanda suka kamu da wannan cutar mashako kimanin 9569 haka kuna 5300 sun sami lafiya ansallame su sunkoma gidajinsu sai kuma kimanin mutane 500 da suka rasa rayukansau