A wani cigaban, kwamishinan labarai na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, da jami’an gudanarwa ma’aikatar sun kai ziyarar aiki ga hukumar ɗab’i ta jihar Kano.
A yayin da yake jawabi ga, kwamishinan da daraktan kula da ma’aikatar, Alhaji Yahaya Muhammad Idris, ya ce hukumar na buƙatar sabbin injina na zamani saboda kasancewarta maɗaba’a mafi daɗewa a jihar nan.
Inda ya buƙaci taimakon ma’aikatar wajen tabbatar da cewa dukkan hukumomi da ma’aikatun jihar Kano sun cigaba da kawo ayyukansu.
Sannann ya miƙa godiyarsa ga kwamishinan bisa ziyarar da ya kawo wa hukumar.
A nasa ɓangaren, kwamishinan tabbatar wa da hukumar ɗab’in cewa za a yi ƙoƙarin samar da kayan aiki na zamani tare da yin roƙo ga hukumomin da ma’aikatun jihar nan da su cigaba da yin hulɗa ta aiki da maɗaba’ar.
Har’ilayau, kwamishinan ya kai makamanciyar ziyarar ga gidan Rediyo Kano.
Kwamishinan ya bayyana dalilin ziyarar tasa da cewa ziyara ce domin sanin halin da gidan rediyon ke ciki da kuma ganin irin ƙalubalen da take fuskanta.
Inda ya buƙaci hukumar gudanarwar gidan da su cigaba da ƙoƙari wajen tabbatar da an samar da shirye-shirye masu inganci.
Sannan kwamishinan ya nuna damuwarsa game da wata ta’ada ta gidajen rediyo a jihar nan da ke ba wa wasu mutane dama su wajen amfani da kalamai na cin zarafi a yayin gabatar da shirye-shiryensu wanda hakan ya saɓawa ƙa’idojin gudanar da kafafen yaɗa labarai.
Shi ma a nasa ɓangaren, manajin daraktan na gidan rediyo Kano, Alhaji Hisham Habib, ya gode wa kwamishinan bisa ziyarar da ya kawo tare da yi masa alkawarin cewa gidan zai yi aiki tuƙuru da ma’aikatar wajen yaɗa labarai.