Rundunar ƴan sandan jihar nan ta yi ƙarin haske akan wani al’amarin da ya faru, a wani ofishinta lokacin da wasu matasa suka kai farmaki da makamai kuma suka yi ta jifa da duwatsu.
Ga bayanin da mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya yi wa manema labarai.
SP Abdullahi Kiyawa ya ƙara jaddada cewa ba za a saurara wa duk wanda ya fito, domin tayar da hankulan jama’ar Kano ba, ko yin ta’ammali da kayan maye, ko aikata fashi da makami ko yin kwace, ko kuma fadan daba.