Kamar yadda hukumar lafiya ta duniya Ke bayyana irin barazanar da mata da kananan yara ke fuskanta na karancin abinci mai gina jiki a nahiyar afirka.
Wata kungiya mai suna Alive&Thrive mai haɗin guiwa da asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF da kuma gwamnatin tarayyar ƙasar nan na gudanar da taron karawa juna sani wanda ya kunshi likitoci da ‘yan jaridu akan hanyoyin da za’a magance matsalar da mata da yara ke fuskanta kan rashin abinci mai gina jiki tin daga matakin farko.
Taron dai ana gudanar da shi ne a yau anan birnin Kano kuma abokin aikinmu Auwal Hussain Adam da ya halarci taron ya samu zantawa da shugaban kungiyar reshan jihar Kano Dr. Ashiru Hamza Muhd akan makasudin shirya wannan taro