Hasashe na nuni da cewa Kamfanoni masu yawa musamman ma matsakaita da kanana za su rufe su bar kasar nan zuwa wata kasa,
saboda matsalolin da suke fuskanta wajen tafiyar da harkokinsu, wannan kuwa ya biyo bayan sanarwar da kamfanonin raba wutar lantarki ya fitar na kara farashin kudin wutar lantarkin daga ranar 1 ga watan Yuli 2023.
Shugaban kungiyar muhalli na kasa, Komrade Onwumere John ya bayyana shirin karin wutar lantarki zai sa wasu harkokin kasuwanci su tsaya, ma’aikata kuma su kara shiga halin ni ‘yasu.
Onwumere ya ce, “Wannan a zahiri ya nuna shugabanni ba su damu kowane irin hali talaka ya shiga ba babu ruwansu.
Shi ma a nashi jawabin, babban jami’i kuma shugaba na kungiyar masu masana’antu ta kasa, Mista Segun Ajayi-Kadir ya bayyana cewa mambobinsu suna ta kokarin yadda za su ci gaba da harkokinsu, amma duk da hakan za a tilastama wasu daga cikinsu ko dai