Ƙasar Burtaniya za ta shirya babban taro irinsa na farko a duniya da zai yi nazari kan amfani da Basira (AI) da aka fi sani da Artificial Intelligence.
Firaminista Rishi Sunak zai tattauna da Joe Biden Fadar White House kan taron a
Mista Sunak na ganin ya kamata Burtaniya ta gudanar da irin wannan taro kasancewarta ta uku a duniya bayan Amurka da China wajen ƙirƙirar fasahar ta AI.
Rahotanni sun nuna cewa Gwamnatin Birtaniya za ta nazarci hanyoyin da ya kamata a bi wajen aiki da wannan fasaha ta fannin tsaro da kuma duba alfanu da tasirin fasahar ke da shi.
Sai dai izuwa yanzu babu karin haske kan mahalarta taron.