Ƙasar Mali ta ce za ta tura tawagar haɗin guiwa da Burkina Faso domin jaddada goyon bayan su ga sojojin da suka yi juyin mulki a ƙasar.
Sanarwa na zuwa ne bayan da shuwagabannin soji na ƙasar Nijar suka yi watsi da umarnin ƙungiyar na mayar da mulki ga hamɓararren shugaban.
Sojojin Nijar sun sanar da rufe sararin samaniyarsu da iyakokin ƙasar, sun kuma ce a shirye suke wajen kare ƙasarsu.
Kawunan ƙasashen ƙungiyar ya rabu kan ɗauka matakin soji a kan Nijar.
Najeriya da Ivory Coast na kan gaba wajen jaddada buƙatar mayar da shugaba Bazoum bisa shugabancin ƙasar.
Sai dai shugabannin mulkin soji na ƙasashen Mali da Burkina Faso sun nuna goyon bayan su ga Sojojin Nijar, sun kuma ce zasu shigar masu faɗa madamar Ecowas ta kai ma Nijar hari.