Dan takarar gwamnan jihar Katsina na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, a zaben da ya gabata, Sanata Yakubu Lado Dan Marke, ya bayyana rashin amincewarsa da sakamakon zaben da hukumar zabe ta bayyana.
Dan takarar gwamna na jam’iyyar ta PDP, ya ce, ya kamata a daina yin zabe kawai a rinka yin nadi, don yana ganin hakan ya fi dacewa.
Sanata Lado Dan Marke, ya ce “‘Yar manuniya ta nuna ko a lokacin yakin neman zabe, domin duk inda jam’iyyar APC ta je kampe ba ta ji da dadi ba saboda mutane sun gaji da ita, amma duk inda PDP ta je maraba ake yi da ita.
Ya ce, su ba za su yi wani abu da zai saba wa doka ba, za su yi abin da doka ta tanada, saboda haka mutane su kwantar da hankulansu za a yi duka abin da ya dace don kwatowa al’ummar jihar katsina hakkinsu.