Home » Katsina: NDLEA Ta Cafke Wasu Mutane 2 Bisa Zargin Safarar Tabar Wiwi

Katsina: NDLEA Ta Cafke Wasu Mutane 2 Bisa Zargin Safarar Tabar Wiwi

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Katsina, ta kama wasu mutane biyu da take zargi da safarar tabar wiwi bayan ta cafke su da kilo 7 na wasu haramtattun kayan maye.

A cewar Kwamandan hukumar Mohammed Bashir Ibrahim, ya ce, tuni hukumar ta gurfanar da wadanda take zargi a gaban kotu.

Manema labarai sun rawaito cewa, wadanda ake zargin Rabi Musa tare da mijin ‘yar uwarta, Suleiman Umar, an kama su ne a Sabon Titin Kwado da ke Unguwar Barhim a cikin birnin jihar Katsina.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, Rabi Musa tana taimaka wa mijinta mai suna Sani wanda a yanzu haka yake sana’ar sayar da kwayoyi.

Kwamandan NDLEA ya yi kira ga iyaye da su tabbatar an gudanar da gwajin gaskiya kan ta’ammuli da miyagun kwayoyi kafin daura aure tsakanin ‘ya’yansu mata da mazajen da suke son aurensu kamar yadda ake yi na gwajin kwayoyin halitta da sauransu.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?