Wasu al’ummar cikin birnin Katsina, Sun bayyana yunkurin kungiyoyin kwadago na NLC da TUC a matsayin abu marar dalili da kuma rashin tausayin da al’umma suke ciki.
Sun bayyana cewa lamarin da ya shafi shugaban kungiyar kwadago a jihar Imo, wanda kungiyoyin kwadagon suka fake dashi abune da ya shafeshi shi kadai, inda suka bayyana cewa bai kamata a ingiza maaikata shiga yajin aikin ba, wanda yin hakan zai kara jefa rayukansu cikin mawuyacin hali.