Ƙoƙarin ƙasar Koriya ta Arewa na harba makami mai linzami da ke ɗauke da tauraron dan’Adam na leken asiri ya gamu da tazgaro, Lamarin ya sa Japan da Koriya ta Kudu umartar miliyoyin mutane su shirya sauya matsugunai.
Kakakin gwamnatin Japan ya ce, gargadin ya fito fili ne bayan tabbatar da cewa makamin ya fada a wani yanki na daban.
Kafar yada labarai ta gwamnatin Pyongyang ta ce, makamin ya fada a cikin teku saboda matsalar da suka samu. Sannan sun ce za su sake aiwatar da wannan gwaji nan ba da jimawa ba.
Amurka ta bi sahun Japan da Koriya ta Kudu wajen Alla-wadarai da wannan gwaji, tana mai cewa yana dauke da makamin da ya saɓawa dokokin Majalisar Dinkin Duniya.