Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da karar da wasu ‘yan jam’iyyar APC uku su ka shigar a gabanta da ke ƙalubalantar cancantar zababben shugaban ƙasa, Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar tasu zaben da ya gabata.
An yanke wannan hukunci ne a ranar 29 ga Maris ɗin wannan shekara, inda aka kotun ta bayyana cewa waɗanda suka shigar da ƙara a gabanta ba su da hurumin yin hakan.
Kotun ta bayyana dalilinta kan wannan watsi da ta yi da ƙarar da cewa waɗanda suka shigar da ƙarar ba sa daga cikin ‘yan takarar fidda gwani na jami’iyar APC, domin haka ba su da ikon ƙalubalantar zaben Tinubu ba.Tun da fari masu shigar da ƙarar dai sun roƙi kotun ne da ta cire sunan Tinubu a matsayin ɗan takara saboda shi ne mafi ƙarancin karancin ilimi cikin waɗanda suka tsayawa takarar shugaban kasar.
A wani hukunci da babbar kotun ta yanke a watan Nuwamba 2022, kan wannan ƙara, Mai shari’a Ahmed Mohammed ya ce wadanda suka shigar da karar sun yi kuskure wajen daukar matakin kuma ba su da hurumin daukar wannan matakin a kan APC.
Wanda hakan ya sa kotun ƙolin sake tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a ranar 17 ga watan Fabrairu da ta gabata.